An kama wani dan kasar Sin yana kokarin arcewa da $.3 miliyan daga Najeriya

An kama wani dan kasar Sin yana kokarin arcewa da $.3 miliyan daga Najeriya

Hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gwamnatin tarayya watau Economic and Financial Crimes Commission, EFCC a turance ta damke wani dan kasar Sin watau China mai suna Li Yanping da makudan kudaden da suka kai Dalar Amurka dubu 300 yana kokarin arcewa da su ya bar kasar.

Sai dai kamar yadda muka samu tuni har hukumar ta EFCC ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotu dake zaman ta a garin Legas inda aka tuhume shi da laifin yin safarar haramtattun kudaden kasar waje.

An kama wani dan kasar Sin yana kokarin arcewa da $.3 miliyan daga Najeriya

An kama wani dan kasar Sin yana kokarin arcewa da $.3 miliyan daga Najeriya

KU KARANTA: Tsohuwa mai shekaru 100 ta musulunta a Abuja

NAIJ.com ta samu cewa sai dai shi Mista Li Yanping din ya musanta zargin da ake yi ma sa wanda wannan ne ma ya sanya alkalin kotun ya umurci a cigaba da tsare shi a gidan yari har sai watan gobe domin cigaba da sharia'ar sa.

A wani labarin kuma, Bayan dogon zama tare da raba dare da aka yi ta yi a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar, kwamitin dake duba da raba albarkatun kasa ga dukkan sassan mulki na kasar watau Federation Account and Allocation Committee (FAAC) ya raba akalla Naira biliyan 647.4 na watan Maris.

Wadannan kudaken kamar yadda muka samu an raba su ne ga Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a matsayin kason su na watan Fabrerun da ya gabata kamar dai yadda aka saba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

NAIJ.com
Mailfire view pixel