Gwamnati ta shiga tattaunawa da Boko Haram game da Yarinyar nan da taki shiga Musulunci

Gwamnati ta shiga tattaunawa da Boko Haram game da Yarinyar nan da taki shiga Musulunci

Tsohon gwamnan jihar Yobe, kuma Sanatan al’ummar gabashin Yobe, Bukar Abba Ibrahim ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da kungiyar Boko Haram don ganin an sako dalibar makarantar Dapchi daya tilo daya rage a hannunsu.

Ita dai wannan daliba mai suna Leah sharibu ta cigaba da zama a hannun yan ta’addan ne biyo bayan kin amincewa da umarnin Boko Haram na yin watsi da addininta na Kiristanci, tare da sauya shi da Musulunci.

KU KARANTA: Kuma dai: Cikin awanni 24 Yan bindiga sun kai hari wani kauye sau biyu, sun kashe 25

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Sanat Bukar yana cewa za’a sako Leah nan bada dadewa ba: “Ina tabbatar ma Sanatoci cewar gwamnati ta fara tattaunawa da yan Boko Haram game da Leah, da ikon Allah zaa sako ta nan bada dadewa ba, tare da sauran yan matan Chibok”.

Gwamnati ta shiga tattaunawa da Boko Haram game da Yarinyar nan da taki shiga Musulunci

Leah.

Hakazalika Sanata Emmanue Bwacha daga jihar Taraba ya bukaci gwamnatin tarayya da masu tattaunawa da Boko Haram cewar su gaggauta yin duk mai yiwuwa don ganin an sako Leah cikin koshin lafiya tare da sauran yan matan Chibok.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

NAIJ.com
Mailfire view pixel