Badakalar Makamai: Jami'an 'yan sanda za su fara binciken gidaje a Abuja.

Badakalar Makamai: Jami'an 'yan sanda za su fara binciken gidaje a Abuja.

A ranar Talatar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta bayar da sanarwa ga mazauna birnin tarayya Abuja akan su mika wuya makaman su da suka mallaka ba tare da ka'ida ba tun kafin lokaci ya kurace mu su.

Kwamishinan 'yan sanda na babban birnin kasar nan, Sadiq Bello, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa ta ranar da ta gabata da cewa, nan ba da jimawa ba jami'ai za su fara bibiyar gida-gida domin kwacen duk wani makami da ba ya da lasisi.

Sufeto Janar na 'yan sanda; Ibrahim Idris

Sufeto Janar na 'yan sanda; Ibrahim Idris

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, tun a ranar 22 ga watan Fabrairu, sufeto janar na 'yan Sanda Ibrahim Idris, ya bayar da umarnin kwato duk haramtattun makamai dake hannun al'umma a fadin kasar nan.

Wannan umarni ya zo ne sakamakon kashe-kashe da ta'addanci da ya yi kamari a fadin kasar nan tun gabanin shekarar nan.

KARANTA KUMA: Tarihin cutar Kanjamau a takaice

Shugaban na 'yan sanda ya na sa ran wannan mataki zai taimaka wajen kawo karshen ta'addanci kafin lokacin zabe na 2019.

NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, duk da kasancewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, anyi cecekuce a taron shugabannin jam'iyyar APC da ya wakana a ranar Talatar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

NAIJ.com
Mailfire view pixel