Shugabanin da suka mulki Najeriya tun 1999

Shugabanin da suka mulki Najeriya tun 1999

Jamhuriya ta hudu a siyasar Najeriya ta fara ne a shekarar 1999 bayan rasuwar shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha a 1998, wanda ya maye gurbin sa, Janar Abdulsalami Abubakar ne yayi shimfidar mayar da Najeriya kan tsarin mulkin demokradiyya a 1999. A yau Legit.ng tayi muku takaitaccen bayanai a kan shugabanin da suka mulki Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu.

1) Olusegun Obasanjo

A yayin da Najeriya ta koma tsarin mulkin demokradiya a 1999, Olusegun Obasanjo ne ya lashe zaben shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP kuma ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayu. Haifafan jihar Ogun wanda ya mulki Najeriya a zamanin sojoji yayi mulki har na tsawon shekaru takwas kafin Majalisar Tarayya na zamaninsa ta taka masa birki a yunkurin sa na zarcewa kan mulki.

A lokacin mulkin sa, an yafewa Najeriya bashin $18bn daga London da Paris Club, ya kuma kafa hukumar EFCC da ICPC don yaki da rashawa. Hakazalika, duk dai a zamanin mulkin sa an kashe wasu manyan 'yan Najeriya sun kamar Alkalin Alkalai Bola Ige; yan siyasa Funsho Williams da Harry Marshall kuma har yau ba'a binciko wadanda sukayi kisar ba.

KU KARANTA: Sauya jadawalin zabe: An bayyana sunayen ‘yan Majilasar Dattawa masu goyon bayan Buhari

2) Umaru Musa Yar'adua

Umaru Musa Yaradua daga shima daga jam'iyyar PDP ne ya maye gurbin Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayu 2007. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bullo da abubuwa 7 da gwamnatin sa zata mayar da hankali a kai. Shine shugaban kasa na farko ya bayyana kadarorin sa ga al'umma ba tare da an tilasta shi ba.

Ya kuma hada gwamnatin hadin gwiwa inda ya kafa Ma'aikatar Neja-Delta kuma ya yi afuwa ga tsagerun Neja-Delta don magance matsalar fasa bututun man fetur da iskar gas. A karkashin mulkin sa ne kuma aka kashe Mohammed Yusuf shugaban kungiyar Boko Haram na farko. Yar'adua ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu na 2010 sakamakon rashin lafiya da ya dade yana fama da ita.

3) Goodluck Jonathan

Goodluck Jonathan ya kasance mataimakin shugaban kasa Yaradua har zuwa 2010 bayan rasuwar maigidansa. Ya kasance shugaban kasa mai rikon kwarya a baya amma ya lashe zaben shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a 2011 amma kuma ya yi mulki zuwa 2015 kafin ya fadi zaben. Ya kirkiro shirin sauya Najeriya, gwamnatinsa ta gina sabbin jami'oin tarayya guda tara, ya gina layukan dogo kuma ya kafa taron yiwa tsarin mulkin kasa garambawul a 2014.

A karkashin mulkinsa ne yan ta'addan Boko Haram suka kwace garuruwa da dama a yankin arewa maso gabas tare da kai hare-haren bama-bamai a wasu jihohin arewa da Abuja. Karkashin mulkin sa ne yan ta'adda suka sace yan matan Chibok 200 kuma har ya sauka ba'a ceto su ba.

4) Muhammadu Buhari

Bayan fadi takaran zabe sau uku, Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar APC a 2015. Tsohon shugaban na mulkin soja ya dare kan mulki ne da niyyar kawo 'Canji' a Najeriya ta hanyar yaki da rashawa, magance matsalar tsaro da kuma farfado da tattalin arzikin Najeriya. Gwamnatin Buhari tayi ikirarin cin gallabar Boko Haram sai dai daga baya yan ta'addar sun sace yan mata 111 daga garin Dapchi duk da cewa an ceto 106 daga cikin su.

A karkashin mulkinsa, rikici tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadiyyar rasa rayyuka da dukiyoyin al'umma da dama. A baya Buhari ya tafi kasar waje na tsawon watanni inda yayi jinya rashin lafiyar da ba'a bayyana ko menene ba kuma a halin yanzu ana tunanin yana da niyyar kara fitowa takara a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel