Boko Haram: Yadda aka kwato biliyan uku a Naira da Daloli daga tsohon hafsan sojan Jonathan

Boko Haram: Yadda aka kwato biliyan uku a Naira da Daloli daga tsohon hafsan sojan Jonathan

- A lokacin mulkin PDP an yi wadaqa da kudaden yaki da Boko Haram

- Wasu 'yan siyasa da ma manyan sojoji sun sace dukkan kudaden

- A kuma wannan lokaci ne mutanen yankin arewa maso gaba suka yi ta rasa rayukansu

Boko Haram: Yadda aka kwato biliyan uku a Naira da Daloli daga tsohon hafsan sojan Jonathan

Boko Haram: Yadda aka kwato biliyan uku a Naira da Daloli daga tsohon hafsan sojan Jonathan

Wani shaidan gani da ido, ya bayyana yadda wani sojan saman Najeriya ya dawo da kudaden da ya sace daga asusun yaki da Boko Haram.

Bayan da aka samu shaidar cewa ya saci kudin da sun kai Naira biliyan biyu da rabi, da ma wasu qarin dala akalla dala miliyan 150 wadanda ya boye a asusun sa na kasashen waje.

Janar mai ritaya, wanda ya rike kujerar babban hafsan sojin samar Najeriya zamanin Godluck Ebele Jonathan, watau Chief of Air Staff, Air Marshal Adesola Amosu, ya dawo da kudaden ne bayan da aka gurfanar da shi gaban kotu, da shaida qarara cewa ya wawashe kudaden.

DUBA WANNAN: Wata sabuwar cuta ta bulla a Kano

A bahasin kotun dai, JAnar din, tare da wasu biyu, Air Vice Marshal Jacob Adigun da Air Commodore Gbadebo Olugbenga sun gurfana ne gaban kotu, kuma sun dawo da kudaden da suka sata a lokutan da shi Amosu ke kan kujera.

An gano ya saci kudaden ne, da zuba su a hannun jari a wasu kamfunnan mai, irinsu Delfina Oil da ma wasu kafafen a kasashen waje, musamman Turai da Amurka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna El-Rufai ya samu sarauta a Kaduna

Gwamna El-Rufai ya samu sarauta a Kaduna

Girma ya karu: An yiwa El-Rufa'i sarauta
NAIJ.com
Mailfire view pixel