Babu wanda ya karbi cin hanci domin canja tsarin zabe – Majalisar wakilai

Babu wanda ya karbi cin hanci domin canja tsarin zabe – Majalisar wakilai

- Mambobin majalisar zartarwa sunce basu karbi cin hanci ba, don su gyara dokar zabe

- Muhammadu Buhari ya kalubalanci tasu dokar ya bukaci a canja da nashi kudirin dokar

- Damburan Nuhu daga jihar kano ya jawo hankalin abokan aikinsa zuwa ga zargin da akeyiwa ‘yan majalisar zartarwa na karbar $30,000 don canja dokar

Mambobin majalisar zartarwa sunce basu karbi cin hanci ba, don gyara dokar zabe.

Kamar yadda kuka sani, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci tasu dokar ya bukaci a canja da nashi kudirin dokar.

Damburan Nuhu daga jihar kano ya jawo hankalin abokan aikinsa zuwa ga zargin da akeyiwa ‘yan majalisar zartarwa na karbar $30,000 don canja dokar, yayi wannan jan hankali ne zaman majalisar a ranar Laraba.

Babu wanda ya karbi cin hanci domin canja tsarin zabe – Majalisar wakilai

Babu wanda ya karbi cin hanci domin canja tsarin zabe – Majalisar wakilai

Wasu daga cikin ‘yan majalisar sunyi korafin cewa wadannan maganganu sun janyo masu matsaloli da dama, inda Damburan Nuhu na jihar kano yace, jama’ar mazabarsa sun fara sanyawa wakilcinsa alamar tambaya, shi kuma Tajudeen Yusuf na Jihar Kogi yace, “wannan rahotanni duk cike suke da karairayi”.

KU KARANTA KUMA: Kyakyawan hoton shugaba Buhari da jikarsa

Shugaban Majalisar Yakubu Dogara, ya mika lamarin ga kwamitin bincike, “Don bawa majalisar shawara akan matakin daya kamata ta dauka; idan ma ta kama mu kai kara kotu”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kaico: Hatsarin Wata Babbar Mota ya muƙurƙushe wasu Motoci 15 a Arewacin Najeriya

Kaico: Hatsarin Wata Babbar Mota ya muƙurƙushe wasu Motoci 15 a Arewacin Najeriya

Kaico: Hatsarin Wata Babbar Mota ya muƙurƙushe wasu Motoci 15 a Arewacin Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel