Babbar magana: Yansanda 13 ne suka taimaka ma yaran Dino Melaya da suka tsere daga Ofishin Yansanda

Babbar magana: Yansanda 13 ne suka taimaka ma yaran Dino Melaya da suka tsere daga Ofishin Yansanda

Rundunar Yansandan jihar Kogi ta tabbatar da rahoton tserewar wasu miyagun mutane guda 2 da suka tabbatar da cewar Sanata Dino Melaye ne ke basu makamai da kudi don su tayar da zauni tsaye.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Ali Janga ne ta bayyana haka a ranar Laraba 28 ga watan Maris, inda yace mutanen guda biyu da suka hada da Kabiru Seidu, inkiya Osama, da Nuhu Salisu inkiya Small, sun arce ne da misalin karfe 3:20 na dare, daga ofishin Yansanda na A dake Lokoja.

KU KARANTA: Ba zan je Kotu ba saboda gwamnan jiharmu ya shirya kashe ni – Inji wani Sanata Ba zan je Kotu ba saboda gwamnan jiharmu ya shirya kashe ni – Inji wani Sanata

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito baya da yaran Melaye, akwai wasu mutane guda hudu da suka hada da Aliyu Isa, Adams Suleiman, Emmanuel Audu da Musa Muhammed, dukkaninsu sun tsere daga ofishin Yansandan.

Sai dai kwamishinan ya bada tabbacin a yanzu haka sun yi ram da yansandan guda 13 da ake zargi da taimaka ma yaran Melaye su tsere, inda yace tuni sun fara shan tambayoyi, don gani yadda aka haihu a ragaya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya karbo bashin kusan Tiriliyan 10 a shekara 3 Inji PDP

Shugaba Buhari ya karbo bashin kusan Tiriliyan 10 a shekara 3 Inji PDP

Satar inna-naha da ake yi a Gwamnatin Buhari ta sa ake cin bashi – PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel