Yadda igiyar leko ta yiwa karen sigari fintinkau ta fuskar illata dan Adam

Yadda igiyar leko ta yiwa karen sigari fintinkau ta fuskar illata dan Adam

Wani sabon bincike ya bayyana cewa, girman ta'ammali da ake yi da igiyar leko a nahiyyar Afirka, Asia da kuma Amurka ta Kudu ya kai wani munzali wanda kafin a kaurace sai an dauki tsawon lokaci.

Mafi akasarin mutane ba su da masaniya akan illar da igiyar leko ke yiwa hunhu na dan Adam. Wannan illa ta maganin Sauro ta zarce irin illar da hayaki na karan sigari keyi.

Yadda igiyar leko ta yiwa karen sigari fintinkau ta fuskar illata dan Adam
Yadda igiyar leko ta yiwa karen sigari fintinkau ta fuskar illata dan Adam

Sandeep Salvi, shugaban cibiyar binciken lafiya kirji ta Chest Research Foundation ya bayyana cewa, kone igiyar leko guda daya ya kan saki kwayoyin cuta na formaldehyde da sai an kone kararen sigari 51 kafin su goga kafada da na igiyar leko.

KARANTA KUMA: Majalisar Tarayya ta jinkirta amincewa da kasafin kudi na 2018 zuwa watan Mayu

Binciken ya tabbatar da cewa, kone igiyar leko guda daya ta kan saki kwayoyi cuta da sai an kone kararen 75 zuwa 137 a bisa ma'aunin gram.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani babban Fasto na kasar Kenya ya bayyana dalilin sa na shafe sama da shekaru goma ba tare da kusantar iyali ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel