2019: Wasu Inyamuran kasar nan sun bayyana Kwankwaso a matsayin ‘Dan takara

2019: Wasu Inyamuran kasar nan sun bayyana Kwankwaso a matsayin ‘Dan takara

- Wasu Inyamurai sun yi kira ga Kwankwaso ya zama Shugaban kasa

- Kungiyar AIPPG tace babu wanda ya dace da Najeriya sai Kwankwaso

- Kwankwaso dai fitar da matsayar ko zai yi takarar Shugaban kasa ba

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wasu Inyamuran kasar nan sun bayyana tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin ‘Dan takarar su na Shugaban kasar Najeriya a zabe na gaba.

2019: Wasu Inyamuran kasar nan sun bayyana Kwankwaso a matsayin ‘Dan takara
Da alamu Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso zai nemi takarar Shugaban kasa

Wata Kungiyar siyasa ta Tarayyar Inyamurai ta AIPPG ta bakin Shugaban ta Lady Rosemary Ukiwe ta bayyana cewa babu wanda ya cancanci ya rike Najeriya irin tsohon Gwamna kuma Sanatan Jihar Kano na yanzu.

KU KARANTA: Kwankwaso ya nuna da gaske yake yi wajen neman kujerar Shugaban kasa

Kungiyar kamar yadda Sakataren ta watau Romanus Azubuike ya bayyana duk Arewacin kasar ba su samu wanda ya dace ya rike Najeriya ba irin Kwankwaso saboda irin namijin kokarin da yayi lokacin yana Gwamnan Kano.

Inyamuran sun nuna cewa tafiyar Kwankwasiyya ita ce ta hada yara da kuma manya don haka su ke ganin ya kamata a ba Kwankwaso wanda mutum ne mai jini-a-jika da kuma shekaru dama ya jarraba sa’ar sa a matsayin Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel