An dauki 'yan bijilanti 1,200 domin maganin barazanar tsaro a jihar Katsina

An dauki 'yan bijilanti 1,200 domin maganin barazanar tsaro a jihar Katsina

Kungiyar 'yan bijilanti a jihar Katsina ta yiwa mutane 1,200 rijista domin taimakawa jami'an tsaro a jihar wajen hana aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

Shugaban kungiyar bijilanti a jihar, Alhaji Abba Mainayara, ya sanar da hakan a ganawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

Tun shekarar 2009, kungiyar Boko Haram take aiyukan ta'addanci da ya yi sanadiyar dubban mutane tare da raba wasu da dama da muhallinsu, a arewacin Najeriya.

An dauki 'yan bijilanti 1,200 domin maganin barazanar tsaro a jihar Katsina
'Yan bijilanti

"Kungiyar bijilanti ta bude ofisoshi a kananan hukumomin jihar Katsina 34. Hikimar yin hakan shine; karfafa tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma," in ji Mainayara.

Sannan ya kara da cewa, "kungiyar mu na aiki kafada da kafada da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), hukumar kula da shige da fice (NIS), da kuma civil defence (NSCDC)."

DUBA WANNAN: Mavrodi, Mutumin da ya gudu da biliyoyin Nairorin 'yan Najeriya ta hanyar MMM, ya mutu

Mainayara ya ce kungiyar su na mika duk mai laifin da ta kama hannun hukumomin tsaron da ya dace tare da bayyana yadda kungiyar ta bullo da tsarin sintiri a fadin jihar domin rage afkuwar aiyukan ta'addanci da kuma hana masu laifi wargi.

Daga karshe, ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta tallafawa kungiyar da ababen hawa domin inganta aiyukanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel