Malaman Addini sun koka kan yadda ake shigo da miyagun kwayoyi cikin Arewa

Malaman Addini sun koka kan yadda ake shigo da miyagun kwayoyi cikin Arewa

- Babban Limamin Masallacin ITN ya nemi a samawa matasa sana’a

- Malamin ya kuma koka da yadda tarbiyya ta lalace yanzu a Kasar

- A hudubar Juma’a ya koka da yadda ake safarar miyagun kwayoyi

A Ranar Juma’ar nan ne mu ka samu labari cewa wani Babban Malamin Addinin Musulunci a Garin Zaria a Jihar Kaduna yayi kira ga Gwamnati ta samawa Matasa a Najeriya sana’a.

Dr. Mustapha Isa Qasim, wanda shi ne babban Limamin Masallacin ITN na Garin Zaria yayi hudubar wannan makon ne a kan yadda tarbiyya ta tabarbare. Babban Malamin yace talauci na cikin abin da ya jawo lalacewar tarbiyya.

KU KARANTA: Abin da ya sa ake zargin Shugaba Buhari da zargin kashe wasu kabilu

Shehin Malamin ya kuma koka da yadda ake shigo da miyagun kwayoyi cikin Arewacin Najeriya. Malamin dai ya yaba da irin kokarin da Jami’an Kwastam su ke yi amma ya nemi Hukuma ta dage wajen kawo karshen harkar kwayoyi a kasar.

Malamin ya nemi Gwamnatin Najeriya ya fadakar da jama’a ta kuma ba aiki da damar koyon sana’a domin su samu abin hannu. Kwanakin baya a Hudubar Malamin ya nemi jama’a su shiga harkar noma gadan-gadan domin kasa ta cigaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel