Masu amfani da wayar salula sun kai kusan miliyan 150 a yau a Najeriya, inji NCC

Masu amfani da wayar salula sun kai kusan miliyan 150 a yau a Najeriya, inji NCC

- Yawan 'yan Najeriya na karuwa, kuma yawancin jama'ar kasar matasa ne, samari da 'yan mata

- An sami karuwar yawan masu amfani da wayar salula da yanar gizo a kasar nan

- Wannan na nufi akwai dumbin riba ga masu harkar wayoyin sayarwa da masu bada layuka

Masu amfani da wayar salula sun kai kusan miliyan 150 a yau a Najeriya, inji NCC
Masu amfani da wayar salula sun kai kusan miliyan 150 a yau a Najeriya, inji NCC

A sabuwar kididdiga da hukumar sadarwa ta NCC ta saki a makon nan, bayanan na nuna cewa, an sami akalla mutum 147,000,000 masu amfani da wayar hannu ta salula a fadin kasar nan, a kan layukan MTN, GLO, 9mobile da Airtel.

Wannan na nufin akwai dumbin riba ga jama'a da kamfanoni masu harkar sadarwa da masu hada-hadarta.

Wanda ya wakilci Executive Vice Chairman na hukumar ta NCC, Prof. Umar Danbatta ne ya byyana hakan a taron baje koli da ake yi yanzu haka a Inugun kudancin Najeriya.

DUBA WANNAN: Yadda ake wa Kiristoci wayo a amshe musu kudi a coci

A cewar Director of Public Affairs, Mr Tony Ojobo mai wakiltar Danbattar, ya kara da cewa, a cikin wadanda ke da wayar, akalla kashi daya bisa biyar suna amfani da hanyar sadarwar zamani ta Intanet a broadband, wanda ya ce hakan yana kara ribanya sosai a kowanne kwata na shekara, kuma yace hakan alheri ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel