An haramtawa Malaman Makarantun kasuwa duba jarrabawar WAEC

An haramtawa Malaman Makarantun kasuwa duba jarrabawar WAEC

- WAEC ta haramtawa Malaman da ba na Gwamnati ba shiga jarrabawa

- Kiristocin kasar sun bayyana cewa su ake kokarin yaka amma a kaikaice

- Wannan mataki bai rasa nasaba da yawan satar amsar da ake yi a Kasar

Mun samu labari daga Jariar Premium Times cewa Hukumar da ke gudanar da jarrabawar kammala Sakandare a kasashen Afrika ta yamma watau WAEC ta kawo wani sabon tsarin da ya jawo hayaniya a wasu bangaren Najeriya.

An haramtawa Malaman Makarantun kasuwa duba jarrabawar WAEC
Kiristocin Najeriya za su yi bore a dalilin sabuwar dokar WAEC

Hukumar WAEC ta haramtawa Malaman Makarantun da ba na Gwamnati ba tsaron jarrabawar WAEC a Najeriya wanda hakan ya Kiristocin Najeriya ke barazanar yin bore da kauracewa jarrabawar gaba daya a dalilin hakan.

KU KARANTA: Gwamnan Kogi ya caccaki Sanata Dino Melaye

Shugaban masu Makarantu a Najeriya Ekaete Ettang ta bayyanawa manema labarai a Garin Jos jiya cewa za su zare hannun su daga harkar jarrabawar WAEC gaba daya don kuwa da su ake. Ettang ta nemi Ma'aikatar ilmi ta shiga maganar.

Dazu dai kun ji labari cewa mai kudin Duniya Bill Gates ya nemi Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dage wajen habaka harkar ilmi da kiwon lafiya inda ya bayyana abin da ya kashe a Najeriya wajen inganta harkar lafiya a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel