Jaririna ya fada masai ne bisa tsautsayi

Jaririna ya fada masai ne bisa tsautsayi

Wata malamar makaranta da ake zargi da jefa jaririnta a cikin masai, ta ce ba da gan-gan ya fada ba, ta ce a bisa tsautsayi ne.

Saidai wasu mutane sun ce matar, Evaline Chesang, ta haifi jaririn amma ta jefa shi a masai sannan ta tsere.

Wasu mazauna gidan da abin ya faru sun ce Malama Chesang ta nemi izinin yin amfani da bankin gidansu, amma bayan ta jima bata fito ba sai suka fara zargin ko wani abu ne ya faru da ita, hakan ya saka su bin sahunta zuwa bandakin.

Jaririna ya fada masai ne bisa tsautsayi
Jaririna ya fada masai ne bisa tsautsayi

Saidai jin motsinsu keda wuya sai ta fito daga bandakin da jini a hannayenta da kuma zaninta amma da suka tambayeta sai ta ce jinin al'ada ne, kamar yadda wata daga cikin mazauna gidan ta fada.

Jami'an 'yan sanda a yankin Mogogosiek a kasar Kenya, sun yi nasarar cafke matar bayan an sanar da su abinda ta aikata.

Sai dai Malama Chesang ta ce, "Jaririn ya fada masan ne bisa tsautsayi, kuma ina jin tsoron sanar da kowa, hakan ya saka ni rugawa gida domin sanar da mahaifiya ta."

DUBA WANNAN: Girma ya fadi: An gurfanar da wani dan shekaru 52 bisa laifin wasa da nonon kwaila

Wasu masu tausayi sun yi nasarar ceto jaririn bayan shafe fiye da sa'a guda wajen budewa tare da shiga masan.

Wani jami'in gwamnati a kasar Kenya, Kipngetich Towett, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewar jaririn na samun kulawa. Kazalika, ya ce, dole su gurfanar da Malama Chesang.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel