Za a cashe a kasar Saudiyya, an gayyato wani fitaccen makidi

Za a cashe a kasar Saudiyya, an gayyato wani fitaccen makidi

A karo na farko a tarihinta, masarautar kasar Saudiyya ta gayyato fitaccen masanin kida (DJ) domin cashewa da kida.

Wannan shine karo na farko a tarihin kasar Saudiyya da aka tabo gayyato makidin zamani domin kawai a sha kida a cashe da rawa.

Shafin Arabian Business dake yanar gizo ya wallafa cewar gidan sarautar Saudiyya ya bayar da sanarwar gayyato shahararren makidi, Armin Van Buuren, zuwa bikin rawa na farko a tarihin kasar.

Za a cashe a kasar Saudiyya, an gayyato wani fitaccen makidi
Yariman saudiyya; Muhammed Bin Abdallah

Za a gudanar da bikin casun ne ranar 17 ga watan Yuni a Birnin tattalin arziki na Sarki Abdallah. Yayin bikin rawar, kasar Saudiyya zata bayyana shirinta na kashe biliyoyin Dalar Amurka domin gina wuraren shakatawa da na wasanni da za a ke gayyato masu nishadantarwa daga kasashen Turai.

DJ Van Buuren, dan asalin kasar Jamus, na rike da kambun gwanayen kidan zamani karo na biyar a jere kamar yadda jaridar DJ mag ta kasar Amurka ta bayyana.

DUBA WANNAN: An kama dalibin makarantar sakandire mai shekaru 15 da bindiga

Ma'aikatar nishadi da walwala ta kasar Saudiyya ta dauki nauyin shirin sannan kamfanin Brackets ya shirya.

Kasar Saudiyya na kawo canje-canje a karkashin shirin yariman kasar mai jiran gado, Mohammed bin Salman da aka fi kira da MBS, na mayar da kasar ta zamani.

Yanzu dai kasar Saudiyya ta fara yin adabo da salon rayuwa irin na 'yan mazan jiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel