Zaa iya dasawa mutum zuciyar Alade - Bincike

Zaa iya dasawa mutum zuciyar Alade - Bincike

Rahotanni sun kawo cewa wani bincike dam asana kimiya suka gudanar ya tabbatar da cewa akwai kamanceceniya tsakanin kwayoyin hallitan jikin dan adam da na Alade.

Harma an tabbatar da cewa anyiwa wani mutum dashen zuciyar Alade. Sannan kuma akayi amfani da bargon Alade ga wasu mutane dake fama da cutar karancin siga a jininsu.

Haka ma mutane da dama da suke dauke da wasu cututukan da suka shafi fatar jiki, anyi musu amfani da fatar Alade, kuma dukkan su sun samu sauki.

KU KARANTA KUMA: Kada ka sake takara – APP ga Buhari

Masanan sun kara da cewar, suna kokarin samar da wasu maguguna da zasu kare mutun, daga daukar wasu cututuka daga jikin Alade, idan har an yimishi dashen wani bangare na Aladen.

A wani lamari na daban Legit.ng ta rahoto cewa jami’an hukumar lafiya a jihar Katsina sun tabbatar da mutuwar mutane takwas sakamakon billar cutar sankarau.

Kwamishinan lafiya ta jihar Katsina, Mariatu Usman ta tabbatar da hakan ta wani sakon waya a ranar Lahadi.

A cewarta, an fara samun faruwar al’amarin da farko a yankin Bugaje karamar hukumar Jibia a ranar 17 ga watan Janairu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel