Kada ka sake takara – APP ga Buhari

Kada ka sake takara – APP ga Buhari

- Jam’iyyar APP ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya sake neman takara a 2019

- Shugaban jam’iyyar na kasa, Ikenga Imo Ugochinyere, yace shugaban kasar ya kammala zagonsa na farko sannan yayi ritaya daga siyasa

- Ya bayyana cewa yan Najeriya sun tsige shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2015 saboda gazawarsa

Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya sake neman takara a 2019.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Ikenga Imo Ugochinyere ya bada shawarar ne a ranar Litinin, 19 ga watan Maris a taron jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa yan Najeriya sun tsige shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2015 saboda gazawarsa, inda ya ce haka za a kora Buhari a 2019 idan ya sake takara domin shima ya gaza.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta yiwa yar kishiyarta duka har lahira

A cewarsa, gwamnatin Buhari yta gaza ta fannin tsaro, tattalin arziki, girmama hakkin biladam, yaki da rashawa da sauransu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa sanannen tsohon dan siyasa a jihar Kano kuma attajirin dan kasuwa, Alhaji Bashir Tofa, ya soki shirin wayar da kan al’ummar Najeriya mai taken ‘Change Begins with me’ Daga kaina canji zai fara.

Alhaji Bashir Tofa, ya ce, kamata ya yi a fara ganin canji daga kan Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da kan mukarraban sa tukunna kafin sauran al’ummar kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel