Sifeto janar ya bayar da umarnin janye jami'an 'yan sanda daga jikin shafaffu da mai

Sifeto janar ya bayar da umarnin janye jami'an 'yan sanda daga jikin shafaffu da mai

- Sifeto janar na 'yan sanda ya umarci dukkan jami'an hukumar da su janye jiki daga wurin duk wani aiki da su ke yiwa wasu mutane na musamman

- Ya bukaci dukkan ma su amfani da lambobin hukumar na musamman su dawo da su

- Sifeton ya bukaci dukkan kwamishinonin jihohin Najeriya da su kafa kwamitin da zai tabbatar jami'an 'yan sanda sun yi biyayya da wannan umarni

Sifeto janar na hukumar 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya umarci dukkan jami'an 'yan sanda dake yiwa 'yan siyasa da shafaffu da mai aiki a fadin kasar nan da su janye jiki, su koma ofis, saboda kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta.

Tun cikin watan Yuni, shugaban 'yan sandan ya ce hukumar ta kammala shiri domin mayar da jami'anta dake yiwa wasu tsirarun 'yan siyasa da shafaffu da mai aiki zuwa bariki, tare da bayyana cewar hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda kara yawan jami'an 'yan sanda da zasu yiwa jama'a aiki.

Sifeto janar ya bayar da umarnin janye jami'an 'yan sanda daga jikin shafaffu da mai
Sifeto janar ya bayar da umarnin janye jami'an 'yan sanda daga jikin shafaffu da mai

Idris ya bayar da wannan umarni ne yau a Abuja yayin wata ganawa da mayan jami'an. Ya ce umarnin ya shafi hatta manyan kamfanonin kasa da kasa dake aiki a Najeriya.

Idris ya kafa kwamitin ko ta kwana karkashin ACP Mohammed Dankwara da zai tabbatar da dukkan jami'an 'yan sanda dake fadin kasar nan sun yi biyayya ga dokar yayin da ya bukaci kwamishinonin jihohi su kafa nasu kwamitocin.

DUBA WANNAN: Ya kai kansa ga hukuma bayan samun katinsa na aiki a sansanin makiyaya

Sifeton ya ce daukan wannan mataki ya zama tilas ne saboda kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta, domin akwai bukatar aikin jami'an ga jama'a.

Kazalika, ya bayyana cewar, masana'antu da manyan mutane dake bukatar tsaro kan iya rubuta takardar bukata hakan zuwa sashen bayar da tsaro na musamman dake hukumar.

Idris ya kara jan kunnen jami'an 'yan sandan a kan kunna jiniya ba bisa ka'ida ba tare gargadin jama'a a kan rufe lambar motoci. Ya umarci ma su rike da lambobin mota da hukumar ke bayarwa na musamman da su dawo da su tare da sake rubuta sabon neman izinin karbar lambar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel