Yarima mai jiran gado : Mutuwa ce kadai zata iya hana mulkin kasar Saudiyya

Yarima mai jiran gado : Mutuwa ce kadai zata iya hana mulkin kasar Saudiyya

- Mohammed bin Salman, yace mutuwa ce kadai zata iya hana shi shugabancin kasar Saudiyya

- kasashen turawa suna daukan Mohammed bin Salman a matsayin mutumin da ya kawo canji a kasar Saudiyya

Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, yace mutuwa ce kadai zata iya hana ci mulkin kasar Saudiyya.

Yarima Mohammed bin Salman, ya bayyana haka ne a wata hirar da yayi da manema labarun gidan Talabijin din CBS a washe garin ranar ziyarar sa ta farko zuwa kasar Amurka.

“Allah na kadai yasan wanda zai dade a duniya, amma idan abubuwa suka tafi kamar yadda aka tsara su, tabbas zan zama shugaban kasar Saudiya,” inji Mohammed bin Salman Salman.

Yarima mai jiran gado : Mutuwa ce kadai zata iya hana mulkin kasar Saudiyya
Yarima mai jiran gado : Mutuwa ce kadai zata iya hana mulkin kasar Saudiyya

Da aka tambaye shi cewa, mai yake ganin zai iya hana shi zama shugaban kasar Saudiya, sai yace, Mutuwa.

KU KARANTA : Ko kun san wacece Hajiya Zainab, tsohuwar matar Dangote?

Tunda Mohammaed Bin Salman, ya samu mukamin yarima mai jiran gado ya fara kawo sauye-sauye al’adu kasar Saudiyya.

Manyan kasashen duniya musamman na turawa suna daukan Mohammaed Bin Salman, a matsayin mutimun da ya kawo wa kasar Saudiyya canji.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel