Mata ne ke girka mani tuwo Inji Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Mata ne ke girka mani tuwo Inji Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

- Sarkin Kano ya bayyana cewa Matan sa su ke masa abinci

- Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana da mata har 4

- Sai dai har yanzu Amaryar ba ta tare tukuna a fadar sa ba

Kwanakin baya Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana wani abin da ba a sani ba game da fadar sa da iyalin sa lokacin da yayi wata doguwar hira da Jaridar FT ta Turai.

Mata ne ke mani girki Inji Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Sarki Sanusi II yace iyalin sa ke dafa masa tuwo

Sarki Muhammadu Sanusi II wanda yake da ‘Ya ya 12 (mata 7 da maza 5) ya bayyana cewa yana da matan aure 4. Sai dai Amaryar ta sa ba za ta tare ba sai bayan ta kammala Jami’ar a Turai sannan za ta shigo cikin fada.

KU KARANTA: Wani tsohon Mataimakin Shugaban kasa ya sha bulala

A tattaunawar da mai martaba yayi, ya bayyana cewa iyalin sa ne su ke dafa masa abincin sa. Bakon da yayi hira da shi ya ga abinci iri-iri wanda su ka hada tuwon shinkafa da waina da dai sauran abubuwan tabawa birjik.

A hirar idan ba ku manta ba Mai martaba Sarkin na Kano ya bayyanawa ‘Dan jaridar cewa daya daga cikin ‘Ya ‘yan sa mata na da burin zama Sarkin Kano nan gaba. Yanzu dai kusan shekaru 3 kenan Sarkin yayi a karaga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel