Jam'iyyar mu ta APC na kan hanyar rushewa in ba a yi hankali ba - Murtala Nyako

Jam'iyyar mu ta APC na kan hanyar rushewa in ba a yi hankali ba - Murtala Nyako

Tsohon gwamnan jihar Adamawa kuma jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Murtala Nyako ya gargadi shugabannin jam'iiyar ta APC da su guji maimaita abun da ya jao rugujewar jam'iyyar PDP a gabanin zaben 2015 ta hanyar tabbatar da yin adalci ga kowa.

Gwamnan kamar yadda muka samu ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ziyarar ta'aziyyar da ya kai wa iyalan tsohon gwamnan jihar Saleh Michika a a ranar asabar din da ta gabata.

Jam'iyyar mu ta APC na kan hanyar rushewa in ba a yi hankali ba - Murtala Nyako
Jam'iyyar mu ta APC na kan hanyar rushewa in ba a yi hankali ba - Murtala Nyako

KU KARANTA: An fara shirin sasanta Buhari da 'yan majalisu

Tsohon Gwamna Nyako din haka zalika ya bayyana cewa hukuncin da jam'iyyar ta APC ta dauka na kin yin zaben shugabannin ta har sai bayan zaba ba zai taba haifar da da mai ido ba domin kuwa idan har aka kai jam'iyyar kotu to za'a rufe jam'iyyar.

A wani labarin kuma, Dandalin siyasa ya fara zafafa a jihar Imo dake yankin kudu maso gabashin kasar nan biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a karshen satin da ya gabata a garin Owerri, babban birnin jihar ta Imo inda wasu jiga-jigan jam'iyyar suka fice daga taron ana tsakar yin sa.

Mun samu dai cewa wadanda suka fice daga taron sun hada da babban jami'in Sakataren gudanarwa na jam'iyyar a mataki na kasa baki daya mai suna Osita Izunaso da kuma zababbun Sanatocin jam'iyyar Ifeanyi Araraume da Benjamin Uwajiumogu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel