Kakakin majalisar jihar Katsina ya kare mutuncin addininsa, ya ki musabaha da mace

Kakakin majalisar jihar Katsina ya kare mutuncin addininsa, ya ki musabaha da mace

A yayin da hoton Aliyu Sabi'u, kakakin majalisar dokoki ta jihar Katsina ke ta yaduwa a fadin kasar nan wanda ya ki yin musabaha da wata mata, ya janyo cece-kuce da tafka muhawarori a yayin da wasu ke kare shi wasu ko suka da caccaka ce kurum tsakanin su da shi.

Wannan hoto da wani matashi mai sunan Na-Allah Muhammad Zagga ya sanya a shafin sa na sada zumunta, inda yake nuna kakakin majalisar cikin murmushi tare da kin sanya hannun sa cikin tafin hannun matar bayan ta nemi su gaisa da shi.

Kakakin majalisar jihar Katsina; Aliyu Sabi'u Ibrahim
Kakakin majalisar jihar Katsina; Aliyu Sabi'u Ibrahim

Kakakin majalisar jihar Katsina ya kare mutuncin addininsa, ya ki musabaha da mace
Kakakin majalisar jihar Katsina ya kare mutuncin addininsa, ya ki musabaha da mace

Wannan matashi dai yayi kaca-kaca da masu goyon bayan wannan abu da kakakin majalisar ya aikata da cewa, 'yan siyasa na shiga rigar addini a wani sa'ilin domin cimma wata manufa amma su kan manta da hakan a yayin da suka gaza sauke nauyin jagoranci da rataya a wuyansu.

KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci dake haddasa ciwon Koda

Yake cewa, da yawan malumma za su yabawa wannan dan majalisa kan wannan abun son a gani da yayi, amma ko kadan ba za su soke shi ba kan gazawar sa a kujerar mulki.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar WAEC ta sauya jadawalin jarrabawar bana ta shekarar 2018 a sakamakon huro wuta da kungiyar kare hakkin musulmi ta yi a ranar Alhamis din da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel