Sunadarin Vitamin D na dakile ciwon Zuciya - Bincike

Sunadarin Vitamin D na dakile ciwon Zuciya - Bincike

A wani sabon bincike da aka wallafa a mujallar Heart Lung and Circulation ya bayyana cewa, sunadarin Vitamin D ya kan iya taimakawa wajen hana kamuwa da wata matsala ta ciwon zuciya bayan ta buga.

Binciken da kwararrun kiwon lafiya suka gudanar ya bayyana cewa, sunadarin Vitamin D ya kan cudanya da wasu kwayoyin halittu na cikin zuciya da zai hana ta kamuwa da wata matsala.

Sunadarin Vitamin D na dakile ciwon Zuciya - Bincike
Sunadarin Vitamin D na dakile ciwon Zuciya - Bincike

An gudanar da wannan bincike a cibiyar lafiya ta Westmead Institute for Medical Research dake kasar Australia.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Ganduje zai kammala ayyukan da gwamnatin Kwankwaso ta gaza a jihar Kano

Jagoran wannan bincike James Chong ya bayyana cewa, amfani sunadarin Vitamin D yana ci gaba da yaduwa a duniya sai dai har yanzu ba a gano ainihin yadda yake taimakon zuciya ba wajen hana kamuwa da cututtuka.

Chong ya kara da cewa, yana sa ran zuwa wani lokaci kankani bincike zai kai ga gano ainihin rawar da sunadarin Vitamin D ke takawa wajen kariya ga cututtukan zuciya.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin Damilola Osinbajo, diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel