An kama wata mata a Katsina bisa zargin kashe diyar kishiyarta

An kama wata mata a Katsina bisa zargin kashe diyar kishiyarta

-An kama wata matar aure, Sahura Musa, mai shekaru 35, bisa zargin kashe diyar kishiyarta ta hanyar jefa ta a rijiya

-Wannan lamari ya faru ne a kauyen Gyaza dake karamar hukumar Dandume, jihar Katsina

- Kotu ta bayar da umurnin a cigaba da tsare Sahura Musa har zuwa ranar 8 ga watan Maris lokacin da za'a fara sauraron karar

An kama wata mata a Katsina mai shekaru 35, Sahura Musa, an tsareta a gidan Yari na Katsina bisa zargin kisan diyar kishiyarta ta hanyar jefata cikin Rijiya. An gurfanar da ita a gaban mai shari’ah Hajiya Fadila Dikko a ranar Talata bisa laifin kisan kai.

An kama wata mata a Katsina bisa zargin kashe diyar kishiyarta
An kama wata mata a Katsina bisa zargin kashe diyar kishiyarta

Sahura, mazauniyar kauyen Gyaza ce dake karamar hukumar Dandume, Jihar Katsina, za’a cigaba da tsareta har zuwa ranar 8 ga watan Maris, shekarar 2018, a lokacin ne kotu zata saurari karar.

KU KARANTA: Sauya sheka: Mutane fiye da 2000 sun bar APC zuwa PDP a jihar Kano

Dan Sanda mai gabatar da kara ya fadawa kotu cewa a ranar 24 ga watan Janairu, shekarar 2018, misalin karfe 8 na dare, wadda ake zargin ta dauki yarinyar ‘yar shekara biyu da haihuwa mai suna, Nana Farida zuwa inda ba wanda ya sani, sai washegari aka gano gawarta cikin Rijiyar makwabta dake kusa dasu.

Hukumar ‘Yan Sanda sun tsaya kan cewa bincike ne ya kaiga Sahura har aka gano abunda ya faru har aka kaiga kamata. Mai gabatar da karar Sifeta Sani Ado, yace ta aikata laifi daya saba ma sashe na 221 na dokar kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel