Gwamnatin APC ta yiwa ta PDP fintinkau ta fuskar rashawa - Secondus

Gwamnatin APC ta yiwa ta PDP fintinkau ta fuskar rashawa - Secondus

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Cif Uche Secondus ya bayyana cewa, tuni 'yan Najeriya suka dawo daga rakiyar gwamnatin APC sakamakon rashin cika alkawurran da dauka yayin da take fafutikar yakin zabe a shekarar 2015.

Secondus ya yiwa wannan ikirari ne yayin ganawa da mambobin jam'iyyar a wata ziyarar aiki da ya kai birnin Dutse na jihar Jigawa a ranar Litinin din da ta gabata.

Yake cewa, jam'iyyar APC ta dauki alkawurra da dama ga al'ummar kasar nan a yayin da take yakin neman zabe, sai dai har yanzu shiru ake ji tamkar an aika Bawa garin su.

Uche Secondus

Uche Secondus

A kalaman sa, "jam'iyyar APC ta sha alwashin habaka tattalin arziki, shawo kan matsalolin tsaro tare da dakile cin hanci da rashawa, sai ko tantama ba bu rashawa ta samu wuri ta yi kaka-gida a gwamnatin APC tun daga sama har tushen ta."

"Akwai matsalolin tsaro a kasar nan, talauci da yunwa kuma sun yiwa al'ummar kasar nan katutu sakamakon yaudara ta gwamnatin APC."

KARANTA KUMA: Sirrika 10 da Kwallon Kashu ya kunsa ga lafiyar Dan Adam

Jaridar Daily Trust ta ruwiato cewa, tawagar shugaban jam'iyyar na PDP ta hadar da; tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau, tsohon shugaba na majalisar dattawa Abdul Ningi, Ambasada Aminu Wali, tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Ali Sa'ad Birnin Kudi da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmad Muhammad.

NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, gwamna Abdulaziz Yari zai shiga tarihi bayan shekaru 22 da kafuwar jihar Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
KARIN BAYANI: Sakamakon zaben gwamnan jihar Osun 2018

KARIN BAYANI: Sakamakon zaben gwamnan jihar Osun 2018

KARIN BAYANI: Sakamakon zaben gwamnan jihar Osun 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel