Hukumar JAMB zata bawa dalibai damar rubuta jarrabawa daga gida

Hukumar JAMB zata bawa dalibai damar rubuta jarrabawa daga gida

- A kokarin da hukumar JAMB ta ke na ganin ta kyautata harkar jarrabawar UTME, hukumar ta ce zata fito da wata sabuwar hanyar fasaha wacce zata bawa dalibai masu rubuta jarrabawar shiga makarantar gaba da sakandare damar yin jarrabawar a gidajen su

Hukumar JAMB zata bawa dalibai damar rubuta jarrabawa daga gida
Hukumar JAMB zata bawa dalibai damar rubuta jarrabawa daga gida

Hukumar JAMB ta ce zata fito da wani tsari wanda zai taimakawa dalibai da suke son zuwa makarantar gaba da secondary damar rubuta jarrabawar UTME daga gidajen su a fadin kasar nan.

Mai magana da yawun hukumar, Dokta Fabian Benjamin, shine ya bayyana hakan a wata zantawa da yayi a wani gidan rediyo jiya a garin Abeokuta.

DUBA WANNAN: Barayi sun farwa ma'aikatan NNPC sun gudu da miliyan 16 a Kano

Ya ce: "Muna kokari wurin ganin mun kawo fasahar da zata taimaka wa dalibai rubuta jarrabawar UTME din daga gidajen su."

Mai magana da yawun hukumar ya kara da cewa, akwai kalubale babba da hukumar ta ke fuskanta musamman ma akan jarrabawar ta UTME, sannan muna kokari mu ga cewa ta kowanne hali idan munga matsala, mu bi hanyar magance ta don tabbatar da cewar daliban sun yi jarrabawar cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

Ya ce: "Hukumar na jinkirta fitar da sakamakon ne saboda, ana bi a hankali domin tabbatar da kawar da duk wata matsala, sanoda koda bayan sun gama jarrabawar ne zaka iya samun wata hanya da aka bi aka yi satar amsa."

Wani masanin na'ura mai kwakwalwa, Damilola Oyeshola, wanda ya kawo shawarar bai wa daliban damar rubuta jarrabawar a gida, ya ce matsalar rashin kayan aikin fasaha a kasar nan shine zai saka fito da hanyar yin hakan yayi wuya. "Daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a kasar nan shine, daliban da yawa basu san yanda ake amfani da na'urar ba," Oyeshola ya ce, akwai bukatar a karfafa hanyar yin amfani da na'ura mai kwakwalwa musamman a cikin kauyuka domin hakan shine zai bada damar fito da hanyar yin jarrabawar a gida.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel