Gwamnatin Kasar Mauritania ta mayar da N92, 520 a matsayin sabon mafi karancin albashi

Gwamnatin Kasar Mauritania ta mayar da N92, 520 a matsayin sabon mafi karancin albashi

Da sanadin Jaridar Leadership mun samu labarin cewa, gwamnatin kasar Mauritania ta bayar da amincin sabon mafi karancin albashin ma'aikata, na biyan dalar Amurka 257 a kowane wata daga shekarar 2019 mai gabatowa.

Hakan ya bayu ne sakamakon fadi tashin da kungiyar kwadago ta kasar tayi shekaru aru-aru da suka gabata, wanda a yanzu hakar ta ta cimma ruwa.

Ma'aikatan Kasar Mauritania sun samu N92, 520 a matsayin sabon mafi karancin albashi
Ma'aikatan Kasar Mauritania sun samu N92, 520 a matsayin sabon mafi karancin albashi

Ministan kwadago na kasar Soodesh Callichurn shine ya bayyana hakan, inda ya bayar da tabbacin cewa ma'aikata za su fara kwankwadar wannan romo a shekarar 2019 mai gabatowa.

KARANTA KUMA: Sirrika 10 da Kwallon Kashu ya kunsa ga lafiyar Dan Adam

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan fa'aida ta karin albashi za ta amfani kimanin ma'aikata 120, 000 na kasar, yayin da ma'aikatan masaka zasu fi kowane murna sakamakon tsawon lokuta da suke batarwa na neman abin sanyawa a baka.

Jaridar Legit.ng ta kuma kawo muku jerin amfani 10 na ganyen Gwaiba ga lafiyar dan Adam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel