Kowa ya bar gida: Na yi nadamar barin Kungiyar Barcelona - Neymar

Kowa ya bar gida: Na yi nadamar barin Kungiyar Barcelona - Neymar

- 'Dan wasan Brazil Neymar ya fara tuntubar Barcelona da sunan kome

- Masu sharhi sun ce Barcelona za tayi watsi da wannan tayi na Neymar

- Hakan zai ba shi saukin zuwa Real Madrid da ke adawa da Barcelona

Mun samu labari kwanan nan daga Rediyo Faransa cewa ya fara kukan barin tsohuwar Kungiyar sa ta Barcelona. 'Dan wasan da yanzu yake jinya yana kokarin komawa kulob din na sa na da. Wasu kuma na ganin dabara ce kurum.

Kowa ya bar gida: Na yi nadamar barin Kungiyar Barcelona - Neymar
Wasu na tunanin Neymar zai yi dabara ya tsere daga PSG zuwa Madrid

Majiyar mu ta Jaridar Mundo Deportivo ta kasar Sifen ta bayyana mana cewa Babban Dan wasan gaban na PSG Neymar na kukan barin Lionel Messi da Barcelona inda yanzu ya fara tuntubar Kungiyar domin yayi kome.

KU KARANTA: Jarumar 'Yar wasa ta yi aure a Ranar Juma'a

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Kungiyar Real Madrid ta yi waje da Kungiyar PSG daga Gasar UEFA ta Zakarun Nahiyar Turai. Yanzu haka dai 'Dan wasan gaban na Brazil ya na jinyar wani aiki ne da aka yi masa a kafa.

Yanzu duka dai ba wuce watanni 7 ba da 'Dan wasan ya kafa tarihi inda ya zama 'Dan wasa mafi tsada a Duniya bayan PSG ta saye sa daga Barcelona. Real Madrid dai a shirye ta ke ta kashe fam Miliyan 400 yanzu kan Tauraron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel