Kasar Birtaniya za gina gidan fursuna na fam 700,000 a Nigeria

Kasar Birtaniya za gina gidan fursuna na fam 700,000 a Nigeria

Gwamnatin tarayyar Birtaniya dake nahiyar Turai ta bayyana fara shirin ta na zuba tsabar kudin da suka kai kusan dala miliyan daya wajen gina sabon bangaren gidan yari a Najeriya.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin sakataren harkokin wajen kasar ta Birtaniya Boris Johnson wanda ya kuma ce akwai yarjejeniyar sauyin gidan yari na dole tsakanin kasashen biyu.

Kasar Birtaniya za gina gidan fursuna na fam 700,000 a Nigeria

Kasar Birtaniya za gina gidan fursuna na fam 700,000 a Nigeria

KU KARANTA: Rahma Sadau ta bayyana yadda ta rasa budurcin ta

NAIJ.com ta samu cewa inda hakan ta tabbata, yarjejeniyar za ta bai wa wasu daga cikin fursunonin da su ka cancanta damar dawowa da su kasar su ta asali domin cigaba da fuskantar hukuncinsu da aka yanke masu.

Kamar kuma yadda muka samu karin bayani, sabon ginin bangaren da kasar ta Burtaniya za ta yi zai dauki gadaje 112 ne kacal kuma ana sa ran za a gina shi ne a gidan yari na Kiri-Kiri da ke jihar Legas.

A wani labarin kuma, Fadar mulki ta kasar Amurka da ake kira da Pentagon dake da mazauni a birnin New York ta ce ta bankado wasu muhimman batutuwan dake nuni da cewa wasu abokan gabar su na shirin kai masu kazamin harin Nukiliya.

Da yake karin haske game da lamarin, mataimakin shugaban jami'an tsaron hadin gwuiwar kasar Janar Paul Selva ya bayyana cewa tabbas wannan tamkar takalar hancin kasar ne kuma ba za su taba bari hakan ta faru ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)

Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)

Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel