Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

- Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

- Tayi wannan bayanin ne yayin da take yin fira da majiyar mu a satin da ya gabata

- Ta ce an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama ne

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood Rahma Sadau ta yi karin haske game da yadda ta rasa budurcin ta kamar dai yadda ta taba bada labarin cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba a watannin baya.

Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta
Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

KU KARANTA: Zakzaky: 'Yan shi'a sun hargitsa garin Abuja

Jarumar dai ta yi wannan karin haske ne yayin da take yin fira da majiyar mu ta Mujallar fim a satin da ya gabata karon farko tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda taje karatu.

Legit.ng ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa maganar da tayi a watannin bayan na cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba wai tana nufin ta taba zina ba ne domin ita hasali ma ba ta taba zina ba tun da Allah ya halicce ta.

Jarumar ta kara da cewa abunda take so ta fadawa duniya shine an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama kuma a lokacin ne ma ta rasa budurcin na ta kamar dai yadda ta fada.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa muhawara ta zafafa a watannin baya lokacin da jarumar ta bayar da ansa ga wani masoyin ta da ya tambayeta matsayin budurcin ta a kafar sadarwar zamani ta Instagram inda ta ba shi ansa da cewar ita ba cikakkiyar budurwa bace.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel