Tsuguno ba ta kare ba: Shugaban Majalisa Saraki zai koma Kotu a makon gobe

Tsuguno ba ta kare ba: Shugaban Majalisa Saraki zai koma Kotu a makon gobe

- An kuma shirya ranar wata shari'a da Shugaba Majalisa Bukola Saraki

- 'Dan takarar PDP a zaben Sanatan Kwara ta tsakiya yana kara a Kotu

- Abdurrazaq na zargin APC da Hukumar INEC da murdiya a zaben 2015

Mun samu labari cewa yanzu haka ana shirin cigaba da shari'a da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a babban Kotun Tarayya da ke Birnin Tarayya Abuja.

Tsuguno ba ta kare ba: Shugaban Majalisa Saraki zai koma Kotu a makon gobe

Za a fara wata shari'a da Bukola Saraki a babban Kotun Tarayya

Labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa a makon gobe ne za a kara zama a Kotu da Bukola Saraki inda 'Dan takarar PDP Abdurrahman Abdulrazaq ke kalubalantar zaben Bukola Saraki a matsayin Sanatan Jihar Kwara ta tsakiya.

KU KARANTA: Sanatan APC ya babbako bashin da APC da PDP ta ci

A farkon makon nan ne Kotu ta sanar da Shugaban Majalisar da kuma Hukumar INEC game da wannan shari'a. Abdulrazaq wanda yayi takarar karkashin PDP ya nemi Kotu ta hukunta Jami'an INEC da kuma Wakilan Saraki da APC a zaben.

Lauyan da ke kare 'Dan takarar PDP Sambo Muritala yana karar cewa an yi muna-muna a wasu wurare a Yankin ihar Kwara lokacin zaben inda yace Wakilan Bukola Saraki da Hukumar INEC sun sabawa ka'idojin zaben da aka gudanar a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bidiyoyin Ganduje da ake fitarwa sharrin ‘Yan Kwankwaksiyya ne kurum inji Sanatan Kano

Abin da ya sa aka saki bidiyoyin batanci na Gwamna Ganduje – Sanata

Abin da ya sa aka saki bidiyoyin batanci na Gwamna Ganduje – Sanata
NAIJ.com
Mailfire view pixel