Yajin Aiki ya janyo rabuwar kawunan Ma'aikata a Jami'ar Ahmadu Bello

Yajin Aiki ya janyo rabuwar kawunan Ma'aikata a Jami'ar Ahmadu Bello

A ranar Talatar da ta gabata ne manyan ma'aikata na jami'ar Ahmadu Bello karkashin kungiyar SSANU, Senior Staff Association of Nigeria, suka shiga cikin rikicin shugabanci akan yanke shawarar janye yajin aiki ko kuma ci gaba da abin su.

Wani jagoran kungiyar reshen jami'ar, Kwamared Iliya Abdurrauf Bello, ya bayar da sanarwa a ranar talatar na janye yajin aikin tare da umartar mambobin kungiyar da su dawo bakin aikin su cikin gaggawa.

Sai dai wata shugabar kungiyar mata reshen jami'ar, Hadiza Kabir, ta bayyana cewa tuni kungiyar ta sallami Kwamared Bello, saboda haka ba ya da ikon kiran wani taro ko kuma zartar da wani hukunci a madadin kungiyar.

Hadiza ta sha alwashin ci gaba da wannan yajin aiki kuma mambobin kungiyar SSANU za su ci gaba da mara baya akan hakan.

Jami'ar Ahmadu Bello

Jami'ar Ahmadu Bello

Manema labarai na jaridar Daily Trust sun yi shaidar yadda mambobin kungiyar suka yi jayayya da juna a babban ofishin jami'ar.

KARANTA KUMA: Rikicin Matasa ya salwantar da rayuka 3 a jihar Filato

NAIJ.com ta fahimci cewa, mambobi magoya bayan Bello sun yi dagiya ta shiga ofisoshin su domin komawa bakin aikin su, yayin da wasu mabobin magoya bayan kungiyar SSANU suka sha alwashin ba bu wani ma'aikaci da zai shiga ofishin sa.

Wannan lamari ya janyo tasku da damuwa a harabar jami'ar dake Samaru a garin Zaria, yayin da ma'aikatan tsaro suka yadu a sassa daban-daban na jami'ar.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, Hukumar Soji kasa ta Najeriya ta kaddamar da wani sabon barikin sojin a jihar Bayelsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Janar Babangida na murnar cika shekaru 77 yau, karanta wani balli na tarihinsa

Janar Babangida na murnar cika shekaru 77 yau, karanta wani balli na tarihinsa

Janar Babangida na murnar cika shekaru 77 yau, karanta wani balli na tarihinsa
NAIJ.com
Mailfire view pixel