Rikicin Matasa ya salwantar da rayuka 3 a jihar Filato

Rikicin Matasa ya salwantar da rayuka 3 a jihar Filato

Mun samu labarin cewa rayuka uku ne suka salwanta a sabon rikicin da ya afku a tsakanin Fulani da Matasan Irigwe na karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an tsinci gawar matasan Fulani biyu da yammacin ranar Litinin din da ta gabata daura da Rafin Bauna na garin Bassa bayan awanni kadan da tsinto gawar wani matashi na Irigwe.

Rikicin Matasa ya salwantar da rayuka 3 a jihar Filato
Rikicin Matasa ya salwantar da rayuka 3 a jihar Filato

Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah reshen jihar Filato, Muhammad Nuru Abdullahi ya bayyana cewa, an harbe wani Ishaq Yusuf mai shekaru 19 yayin da aka tsinto gawar wani Abubakar Shehu mai shekaru 22 bayan an binne sa a wani tsukukun rami.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari da Bukola Saraki yayin taya kasar Ghana murnar zagayowar ranar samun 'yanci

Yake cewa maharan sun kuma salwantar da rayukan shanu 31 tare da raunata takwas.

Babban ma'aikacin dakaru mai hulda da manema labarai, Manjo Adam Umar, shine ya bayar da rahoto na tabbacin wannan kashe-kashe, inda yace an ci gaba da kulawa da wadanda suka raunata a gadajen asibiti.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Ghana domin taya murnar cikar ta shekaru 61 da samun 'yancin kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel