Afenifere da kungiyar CDHRH sun mayar da martani akan maganar da Buhari yayi akan rikicin Taraba

Afenifere da kungiyar CDHRH sun mayar da martani akan maganar da Buhari yayi akan rikicin Taraba

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni

- Afenifere ta CHDR sun soki Buari akan kalaman da yayi game da kashe-kashen da aka yi a jihar Taraba

Kungiyar Afenifere da kungiyar kare hakikin dan Adam (CDHR), sun soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan kalaman da yayi game da kashe-kashen da aka yi a jihar Taraba a lokacin da ya ziyarci jihar a ranar Litinin.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a lokacin da ya ziyarci jihar Taraba ya ce, adadin mutanen da aka kashe a rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a yankin Mambilla dake jihar Taraba, sun fi adadin mutanen da aka kashe a jihar Benuwe da Zamfara.

Mai magana da yawun bakin kungiyar Afenifere, Yinka Odumakin, ya kalubalanci shugaba Buhari, ya bayyana adadin masu laifi da aka kama ba adadin mutanen da aka kashe ba.

Afenifere da kungiyar CDHRH sun mayar da martani akan maganar da Buhari yayi akan rikicin Taraba
Afenifere da kungiyar CDHRH sun mayar da martani akan maganar da Buhari yayi akan rikicin Taraba

“Aikin shugaba shine kare rayuka da dukiyoyi mutanen sa, ba wai ya rika bayyana wuraren da aka fi yin kashe-kashe a cikin kasar sa ba.

KU KARANTA : Rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni – Buhari

“Masu laifi nawa kama kama, kuma wani kotu aka kai su? Wannan sune maganganun da ya kamata su fito daga bakin shugaban kasa,"inji shi.

Shugaban kungiyar CDHR, Malachy Ugwummadu, Ya ce kalaman da shugaba Buhari yayi jihar Taraba ya nuna rashin iya siyasar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel