Trump yana neman sake jefa duniya cikin rikici

Trump yana neman sake jefa duniya cikin rikici

- Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya kuduri aniyar mai da ofishin jakadancin kasar dake birnin Tal Aviv a kasar Isra'ila zuwa birnin Kudus

- Trump ya bayyana cewa in dai kudurin sa ya tabbata na mai da ofishin zuwa birnin Kudus to zai kokarin halartar bikin bude ofis din

- Sai dai hakan ya kawo cece-kuce a cikin inda da yawa ake ganin hakan zai kara jefa duniya cikin rikici

Trump na neman kara jefa duniya cikin rikici
Trump na neman kara jefa duniya cikin rikici

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana kudurinsa na halartar taron bude ofishin jakadancin Amurka a kasar Isra’ila wanda za'a tashe shi daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus.

DUBA WANNAN:

Bayan ganawa da sukayi a kasar Amurka da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya gana da shugaba Donald Trump bayan haka shugaban ya yi magana da ‘yan jarida, ya bayyana cewa Kudus ce helkwatar Isra’ila ya kuma ce ofishin jakadancin Amurka zai tashi daga Tal Aviv ya koma kudus.

Trump ya bayyana cewa in dai kudirin su ya tabbata na mai da ofishin zuwa kudus to zai kokarin halartar bikin bude shi.

Ya yi shirin zaman lafiya a gabas ta tsakiya, in da bayyana janye maganar matsalar kudus a teburin sulhu. Wanda hakan ya rage matsalolin da kasar ke fuskanta na samun zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel