Yadda gawa ta farfado bayan likitoci sun tabbatar da ya mutu

Yadda gawa ta farfado bayan likitoci sun tabbatar da ya mutu

- Wani mutum mai sun Himanshu Bharadwaj ya samu raunuka sosai dalilin wata mumumman hatsarin mota da ya yi

- Bayan an garzaya dashi asibiti don jinyar sa, likitoci sun duba shi inda suka sanar da cewa ya mutu don babu alamun numfashi a tare dashi

- Bayan ya kwana a dakin ajiye gawa, an fito dashi don fede shi a gano takamamen dalilin mutuwar ta sa sai kuma aka gano ya fara numfashi

Wani mutum mai suna Himanshu Bharadwaj wanda ya yi hatsarin mota kuma likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu ya farfado kafin likitocin su kai ga tsaga gawarsa sa don gano ainihin dalilin mutuwar sa kamar yadda akeyi a wasu kasashen duniya.

An dai gano yana nan da ran sa bayan ya kwana a dakin ajiye gawawaki na asibitin da ke Nagpur na kasar Indiya. Yan uwan sa sun ce wannan dai wani abin al'ajabi ne daga Ubangiji bayan likitan da ke gudanar da bincike kan gawawaki ya fada musu cewa ya gab da fara tsaga gwar ne ya gano yana da rai.

Yadda gawa ta farfado bayan likitoci tabbatar da ya mutu
Yadda gawa ta farfado bayan likitoci tabbatar da ya mutu

KU KARANTA: Labari da duminsa: Majalisa ta umurci Ministan Zirga-Zirgan Jiragen Sama ya bayyana gaban ta

A nan take akayi amfani da na'uran taimakawa dan adam nunfashi don farfafo dashi kuma aka garzaya da shi wani dakin kulawa da marasa lafiya bayan an gano cewa bai mutu ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A waje kuma, al'umma sunyi cincirindo inda suke gudanar da zanga-zangan nuna kin amincewa da abin da suka bayyana a matsayin sakaci daga ma'aikatan asibitin.

Wani likita mai suna Dr. Gedam da ke asibitin yankin Chindwara ya yi bayanin cewa "huhun mutumin na da matsala ne shi yasa ba'a iya gane cewa yana numfashi ba' hakan ne yasa aka sanar da cewa ya mutu."

Gedam ya kara da cewa, "A wasu lokuta, musamman ga wadanda kwakwalwar su ta bugu, zuciya da huhu suna iya dena aiki na dan wani lokaci, kuma hakan ne ya faru shi yasa akayi tsamanin ya mutu ne.

"Har yanzu kwakwalwar sa bata farfado ba, hakan ya sa muka tura shi asibitin Nagpur don ba mu da kayan aikin da zamu iya yi masa aiki."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel