Ta nemi kotu ta raba aurensu saboda yunwa

Ta nemi kotu ta raba aurensu saboda yunwa

- Wata mata ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta saboda rashin abinci

- Matar, Aisha Muhammad, ta zargi mijinta da rashin kulawa da kuma wofantar da ita na tsawon watanni

- Alkalin Kotun, Dahiru Lawal, ya umarci mijin matar, Ahmadu Audu, da ya biya ta N10,000

Wata mata, Aisha Muhammad, ta maka mijinta a gaban kotun magajin gari dake Kaduna bisa zargin sa da yi mata horon yunwa.

Aisha ta shaidawa kotu cewar mijinta, Ahmadu Audu, ba ya iya ciyar da ita. Sai dai kullum ya ce ta je gidan iyayen sa ta ci abinci har tsawon kusan shekara guda, dalilin da ya saka ta yin yaji, ta koma gidan iyayen ta.

Ta nemi kotu ta raba aurensu saboda yunwa

Ta nemi kotu ta raba aurensu saboda yunwa

"Ba zan iya zama da yunwa ba, shi yasa na koma gidan iyayena tun watanni bakwai da su ka wuce," Aisha ta shaidawa kotu.

DUBA WANNAN: Muna kara baza komar mu a fadin Najeriya domin dakile aiyukan ta'addanci - Buratai

A saboda haka ne ta bukaci kotun ta raba aurenta da mijinta tunda ba zai iya kulawa da ita ba.

Sai dai, Audu, ya ce yana kaunar matar sa, tare da shaidawa kotu cewar matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasa ya jawo hakan.

Alkalin kotun, Dahiru Lawal, ya umarci Audu ya biya Aisha N10,000 bisa wofantar da ita da ya yi na tsawon lokaci tare da basu damar yin sulhu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya

Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya

Wani miji ya silale cikin asibiti kawai domin tarawa da matarshi mai jinya
NAIJ.com
Mailfire view pixel