Zaben 2019: Gwamnonin PDP sun shirya fiddo Dankwambo a matsayin magajin Buhari

Zaben 2019: Gwamnonin PDP sun shirya fiddo Dankwambo a matsayin magajin Buhari

Wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi wani taron sirri a daren ranar Lahadi a can garin Gombe bayan kamma taron majalisar zartarwar jam'iyyar da ya gudana a gidan gwamnatin jihar ta Gombe.

Kamar dai yadda muka samu da majiyoyin mu kuma, gwamnonin sun tattauna ne a kan yadda za su fito da gwamnan jihar ta Gombe da yanzu haka yake kare wa'adin mulkin sa a shekarar 2019 domin ya gwabza da shugaba Buhari.

Zaben 2019: Gwamnonin PDP sun shirya fiddo Dankwambo a matsayin magajin Buhari

Zaben 2019: Gwamnonin PDP sun shirya fiddo Dankwambo a matsayin magajin Buhari

KU KARANTA: Yan sanda sun kama mahaukacin karya da bindiga a Legas

NAIJ.com ta samu haka zalika cewa wasu shugabannin jam'iyyar ta PDP daga wasu jahohin kasar ma dai sun samu halartar taron.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Emmanuel Udom (Akwa Ibom), Benedict Ayade (Cross River), Darius Ishaku (Taraba), Ibrahim Dankwambo (Gombe)Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Ayodele Fayose (Ekiti), Ifeanyi Okowa (Delta).

A wani labarin kuma, Kasar tarayyar Amurka ta bayyana cewa ko shakka babu idanun ta yana kan kasar Najeriya musamman ma wajen yadda za ta gudanar da zabukan ta na shekarar 2019 mai zuwa cikin ingantaccen yanati da tsafta duba da muhimmancin kasar ga zaman lafiyar nahiyar ta Afrika.

Wannan dai ya fito bakin Sakataren harkokin wajen kasar ne Mista Rex Tillerson yayin ziyarar da ya kawo ta aiki zuwa nahiyar ta Afrika kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari na Samun Matsin Lamba Daga makusantanshi akan Mayarda Lawan Daura Shugaban DSS

Buhari na Samun Matsin Lamba Daga makusantanshi akan Mayarda Lawan Daura Shugaban DSS

Buhari na Samun Matsin Lamba Daga makusantanshi akan Mayarda Lawan Daura Shugaban DSS
NAIJ.com
Mailfire view pixel