Halin da Najeriya zata shiga muddin shugaba Buhari bai koma mulki ba - Gwamna Sani Bello

Halin da Najeriya zata shiga muddin shugaba Buhari bai koma mulki ba - Gwamna Sani Bello

- Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya ce 'yan Najeriya ba zasu taba nadamar sake zaben shugaba Buhari ba

- Ya bayyana cewar tattalin arzikin Najeriya zai koma gidan jiya matukar Buhari bai koma mulki ba

- Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su bawa shugaba Buhari goyon baya dari bisa dari

Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya bawa 'yan Najeriya tabbacin cewar ba zasu taba yin nadamar sake zaben shugaba Buhari ba a 2019. Ya bayyana cewar sake zaben shugaba Buhari zai kare dinke Najeriya.

Kazalika ya bayyana cewar rashin zaben shugaba Buhari zai mayar da tattalin arzikin Najeriya cikin halin ni-'ya-su.

Halin da Najeriya zata shiga muddin shugaba Buhari bai koma mulki ba - Gwamna Sani Bello

Gwamna Sani Bello

Gwamnan na wadannan kalamai ne yayin da yake karbar bakuncin mutanen Kontagora a gidan gwamnatin jihar dake garin Minna. Ya shaidawa bakin nasa cewar goyon bayan da ya bawa shugaba Buhari sakamako ne na irin aiyukan alheri da ya shimfida a jihar.

DUBA WANNAN: Abu daya da har yanzu nake nadama a rayuwa - Obasanjo

Naij.com, ciki daya daga cikin labaranta ta shaida maku cewar wasu matasa daga kabilun Urhobo da Isoko a jihar Delta sun bayyana goyon bayansu ga takarar shugaba Buhari a zaben 2019.

Matasan sun bayyana cewar su na goyon bayan Buhari ne saboda dagewar sa a kan yaki da cin hanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kaico: Aukuwar wani Hatsarin Jirgin kasa ta yi matukar muni da rayuka suka salwanta, fiye da 70 sun jikkata

NAIJ.com
Mailfire view pixel