Sheik Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnatin Bauchi game da yi wa darika katsalandan

Sheik Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnatin Bauchi game da yi wa darika katsalandan

Gidauniyar itaccen malamin islama din nan kuma jagoran darikar tijjaniya a Najeriya watau Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gargadi hukumar dake kula da harkar ilimin bai daya watau Universal Basic Education Board (SUBEB) a turance ta jihar Bauchi game da yi wa makarantun allo na zamani katsalandan.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan dake kula da harkokin yada labarai na gidauniyar Malam Ahmad Muhammad Saka ya fitar inda ya yi hasashen babban rikici idan har hukumar ta dage kan sai ta hana yin wazifa da kuma salatul fatihi a makarantun.

Sheik Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnatin Bauchi game da yi wa darika katsalandan
Sheik Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnatin Bauchi game da yi wa darika katsalandan

KU KARANTA: Jami'an kwastam sun kama shikafa buhu 460 mai guba a Arewa

Legit.ng ta samu cewa sanarwar ta kuma bayyana cewa makarantun da gwamnatin tarayya ta gina a jihar dukkan su an yi su ne saboda darajar Sheikh Dahiru Bauchi din don haka bai kamata ba yanzu kuma gwamnatin jihar ta nemi yi masu shishshigi da katsalandan.

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ikirarin cewa kiristoci da kuma wadanda suka fito daga kudancin Najeriya ne suka fi shanawa a wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari sabanin yadda 'yan kasar ke tsammani.

Farfesa Osinbajo yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan jarida tare kuma da ma'abota anfani da kafar sadarwar zamani a cikin karshen satin nan a jihar Legas.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel