Kiristoci da 'yan kudu sun fi cin moriyar gwamnatin Buhari - Inji Osinbajo

Kiristoci da 'yan kudu sun fi cin moriyar gwamnatin Buhari - Inji Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ikirarin cewa kiristoci da kuma wadanda suka fito daga kudancin Najeriya ne suka fi shanawa a wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari sabanin yadda 'yan kasar ke tsammani.

Farfesa Osinbajo yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan jarida tare kuma da ma'abota anfani da kafar sadarwar zamani a cikin karshen satin nan a jihar Legas.

Kiristoci da 'yan kudu sun fi cin moriyar gwamnatin Buhari - Inji Osinbajo
Kiristoci da 'yan kudu sun fi cin moriyar gwamnatin Buhari - Inji Osinbajo

KU KARANTA: Obasanjo ya labarta wata tsiya da ya shuka a shekarun baya

Legit.ng dai ta samu cewa mataimakin shugaban kasar ya bayar da hujjar tabbacin hakan ne inda ya ce akwai musulmai 18 da kuma kiristoci 18 a cikin ministocin Najeriya din to amma kuma Sakataren gwamnati da kuma shugabar ma'aikatan kasar dukkan su kiristoci ne.

A wani labarin kuma, Gidauniyar itaccen malamin islama din nan kuma jagoran darikar tijjaniya a Najeriya watau Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gargadi hukumar dake kula da harkar ilimin bai daya watau Universal Basic Education Board (SUBEB) a turance ta jihar Bauchi game da yi wa makarantun allo na zamani katsalandan.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan dake kula da harkokin yada labarai na gidauniyar Malam Ahmad Muhammad Saka ya fitar inda ya yi hasashen babban rikici idan har hukumar ta dage kan sai ta hana yin wazifa da kuma salatul fatihi a makarantun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel