Da kyar na sha, ya fi da kyar aka kama ni: Hotunan shahararren dan siyasan Kano da ya tsira da harbin bindiga daga wajen masu garkuwa da mutane

Da kyar na sha, ya fi da kyar aka kama ni: Hotunan shahararren dan siyasan Kano da ya tsira da harbin bindiga daga wajen masu garkuwa da mutane

Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai ya yi, inji Hausawa, bugu da kari mai ganin sai ya gani, ko ana daka shi a turmi, tamkar hakan ne ta kasance da Alhaji Ibrahim Al’Amin Little.

Idan za’a tuna a farkon makon data gabata ne wasu masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna suka yi yunkurin sace shahararren dan siyasan jihar Kanon a lokacin da ya fito daga gonarsa a birnn gwari, inda suke bude masa wuta.

Da kyar na sha, ya fi da kyar aka kama ni: Hotunan shahararren dan siyasan Kano da ya tsira da harbin bindiga daga wajen masu garkuwa da mutane
Tawagar Kwamishina tare da Little

KU KARANTA: Don bukatar kashin kai wasu Kwamishinoni na amfani da tsafe tafe wajen juya gwamnansu

Sai dai abinka da mai tsawon kwana, Ibrahim tare da direbansa sun tsira da ransu bayan sun shige motarsu, suka kuma tuko har zuwa cikin garin Kaduna, kai tsaye sai Asibiti, inda suka samu kulawa.

Hotunan halin da Ibrahim ke ciki sun bayyana ne yayin da kwamishinan ayyuka na musamman Abdullahi Abbass ya kai masa ziyarar jajantawa a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Da kyar na sha, ya fi da kyar aka kama ni: Hotunan shahararren dan siyasan Kano da ya tsira da harbin bindiga daga wajen masu garkuwa da mutane
Ziyarar

Tun bayan komawarsa jihar Kano, jama’a na ta tururuwa zuwa gidan Ibrahim Little don jajanta masa, daga cikin wadadanda aka hangi keyarsu sun hada da shugaban karamar hukumar Gwale, Kahild Ishak da mataimakin shugaban karamar hukumar Nassarawa Muhammad Shehu Tudun wada.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel