An raunata mutum 1 a harin fadar 'White House' ta Donald Trump

An raunata mutum 1 a harin fadar 'White House' ta Donald Trump

Legit.ng ta samu rahotanni da sanadin Jaridar The Punch cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne jami'an tsaro suka takaita zirga-zirga tare da dakile duk wata hanya dake farfajiyar fadar White House sakamakon sautin harbe-harbe na bindiga.

Hukumar leken asiri ta kasar Amurka da ta bayyana a shafin ta na twitter cewa, ta fara gudanar da bincike sakamakon rahotanni na wani mutum da ya raunata kan sa da harsashi na bindiga daura da katangar Arewa a fadar White House.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi sa'a shugaban kasar Donald Trump, ba ya cikin fadar a yayin da wannan lamari ya afku, inda fadar ta bayyana cewa ya tafi hutun karshen mako a wani gidan sa na Mar-a-Lago dake birnin Florida a kasar.

Donald Trump
Donald Trump

Manema labarai dake ta watso rahotanni daga cikin fadar ta White House sun bayyana cewa, tuni suka nemi mafaka a cikin ta, yayin da motocin jami'an tsaro da kuma na agajin gaggawa suka zagaye fadar cikin kankanin lokaci.

KARANTA KUMA: Al-Qur'ani shine babban Kundi mai koyar da zaman Lafiya - Buhari

Sai dai wannan tashin-tashin a fadar ta White House ba sabon abu bane, domin kuwa a ranar 23 ga watan Fabrairu, an damke wata mata da ta sukwano motar ta kuma ta dankari wani shinge na jami'an tsaro daura da fadar ta shugaban kasa.

An kuma ci gaba da samun mutane daban-daban a yayin yunkuri na tsallaka katangar fadar kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaba Buhari ya nemi kasar Birtaniya ta tazorta shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kuma mataimakin sa, Ike Ekweremadu, sakamakon mallakar wasu kadarori na makudan kudade a birnin Landan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel