Rundunar Sojin kasa ta damke wasu makiyaya 3 a jihar Nasarawa

Rundunar Sojin kasa ta damke wasu makiyaya 3 a jihar Nasarawa

A sakamakon ci gaba da gudanar da atisayen dakarun sojin kasa mai taken Tseren Kyanwa, sun yi nasarar cafke wasu sakakkun shanu yayin da suke kiwo cikin gonakin mutane a kauyukan Yeas, Kaseyo da kuma Ukaa na karamar hukumar Awe ta jihar Nasarawa.

A yayin haka kuma, dakarun sun yi nasarar damkar wasu makiyaya tare da makamai yayin da suke kiwon shanu su wajen barnatar da amfanin gona da gangan na manoma.

NAIJ.com ta samu wannan rahoto ne da sanadin shafin sada zumuntar facebook na rundunar sojin kasa ta Najeriya, inda dakarun ta suka yi nasarar cafke wannan makiyaya yayin sintiri a yankunan Ayimalo, Tomata, da kuma Kwantan Sule.

Makiyaya 3 da rundunar Sojin ta Damke

Makiyaya 3 da rundunar Sojin ta Damke

Rundunar dai ta bayyana cewa, ta mika wannan 'yan ta'adda zuwa ga hukumar 'yan sanda domin ci gaba da hukuncin da ya dace.

KARANTA KUMA: Al-Qur'ani shine babban Kundi mai koyar da zaman Lafiya - Buhari

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin bincike kan Bukola Saraki da Ike Ekweremadu, dangane da yadda suka mallaki wasu manyan kadarori na makudan dukiya a birnin Landan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sallar idi: Sanata Rabiu Kwankwaso yayi sallah a Kudancin Najeriya

Sallar idi: Sanata Rabiu Kwankwaso yayi sallah a Kudancin Najeriya

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso yayi sallah a Jihar Edo
NAIJ.com
Mailfire view pixel