An bude sashen koyar da kasuwanci a Jami'ar Bayero da Dangote ya gina

An bude sashen koyar da kasuwanci a Jami'ar Bayero da Dangote ya gina

- Alhaji Aliko Dangote ya gina sashin koyar da kasuwanci da sana'o'i a Jami'ar Bayero da ke Kano

- Dangote ya bayyana cewa ingantacen ilimi ne kashin bayar ci gaban ko wane kasa kuma yana fatan cibiyar za ta bayar da gudunmawa wajen gina matasan nahiyar Afirka

- Babban bako a taron, Sarkin Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yabawa Dangote bisa gudunmawar da ya ke bayar wa wajen tattalin arzikin Najeriya

A jiya Juma'a ne aka kaddamar ta sashen koyar da dabarun kasuwanci a Jami'ar Bayero da ke Kano don ya zama wajen koyan ilimin kasuwanci da sana'o'i ga dalibai daga dukkan sassan Najeriya Najeriya.

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II na biyu ne ya kaddamar da ginin wanda ya kunshi ajujuwa, ofisoshi, wuraren cin abinci da sauran su.

Dangote ya gina sashin koyar da ilimin kasuwanci a BUK
Dangote ya gina sashin koyar da ilimin kasuwanci a BUK

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa attajirin dan kasuwar Afirka, Alhaji Aliko Dangote ne ya dauki alkawarin gina cibiyar ne yayin da ya hallarci wani bukin yaye daliban jami'ar ta BUK tun zamanin da Farfesa Attahiru Jega ke jagorancin jami'ar, kuma gashi yanzu ya cika alkwarin da ya dauka.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun dakile yunkurin wata hari da 'yan bindiga suka kai Jihar Zamfara

A jawabin da ya yi jiya wajen kaddamar da taron, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana gamsuwar sa kan yadda aka gudanar da aikin, sannan ya bukaci dalibai da ma'aikatan jami'ar su mayar masa da tukwuici wajen jajircewa don ganin sashin ya bayar da gudunmawa sosai wajen habbakar kasuwanci a nahiyar Afirka.

Ya bayyana cewa ingantaciyar ilimi ita ce kashin bayar tattalin arziki da kuma cigaba a kowane kasa kuma yana fata cibiyar za ta zama abin alfahari wajen koyar da matasa kasuwanci.

Sarki Sanusi ya yabawa Dangote bisa irin gundunmawar da ya ke bayar wa wajen cigaban tattalin arzikin Najeriya da hanyoyi daban-daban kuma ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da yanayi mai kyau da zai sanya yan kasuwa bayar da gudun mawar su.

Shugaban jami'ar, Farfesa Muhammad Bello Yahuza ya yabawa Dangote bisa ayyukan alkhairi da ya ke gudanarwa a jami'ar kuma ya bashi tabbacin cewa jam'ar za tayi amfani da sashin don bayar da gudunmawar su ga al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel