Da sai mun iya hana harin Dapchi - Peace Corps ga Buhari

Da sai mun iya hana harin Dapchi - Peace Corps ga Buhari

A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar tsaro ta Peace Corps, ta ke rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan ya sake nazari kan shawarar sa ta kin amincewa da hukumar cikin doka kamar yadda majalisar zartaswa ta bukata.

Kwamandan hukumar, Mista Dickson Akoh, shine ya yi wannan kira a taron amintattu da zaman majalisa da aka gudanar a babban birni na tarayya.

Akoh ya yi bayanin cewa, daya daga cikin manufofin hukumar shine gudanar da aikace-aikacen tsaro a makarantu da kwalejan ilimi domin wanzar da zaman lafiya, wanda da yanzu harin Dapchi na jihar Yobe bai afku ba.

Peace Corps
Peace Corps

Ya ci gaba da cewa, su na bukatar shugaba Buhari ya shigar da su cikin dokar kasa, idan ba don wani dalili ba, sai domin samar da abin yi ga matasa wanda yana daya daga cikin alkawuran sa na a lokacin yakin neman zabe.

KARANTA KUMA: Wani Dattijo ya yi Odar gubar Bera tun daga kasar Sin domin Kashe Iyayen sa

Da wannan ne Kwamandan yake rokon shugaba Buhari akan ya kara duba a gare su, tare da jaddada cewa akwai makamanciyar hukumar a kasashen Amurka, Canada, Banglasdesh da sauransu.

Kwamandan ya kara da cewa, manufar hukumar ta Peace Corps ba ta ci karo da kowace hukuma sabanin dalilin shugaba Buhari na rashin amincewa da ita.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Kasar Thailand ta soki gwamnatin shugaban kasa Buhari sakamakon rushewar manyan kamfanonin shinkafa na kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel