Yadda hadimi ya boye makudan biliyoyin da ake zargi na Jonathan ne

Yadda hadimi ya boye makudan biliyoyin da ake zargi na Jonathan ne

- Ana ta qara samun bayanai kan irin satar da aka tafka a lokacin mulkin PDP

- An bayyana yadda wani hadimi ya boye kudade a dakin Jonathan

- PDP na kokarin sake dawowa mulki a 2019

Yadda hadimi ya boye makudan biliyoyin da ake zargi na Jonathan ne
Yadda hadimi ya boye makudan biliyoyin da ake zargi na Jonathan ne

An dade ana bankado manya-manyan badakaloli da aka tafka a lokacin mulkin Jonathan, manya daga cikinsu sune na Dasuki, Diezani da Dame Patience, uwargidan shugaba Jonathan. Sai dai ba safai akan ji ko shi kansa oga ya wawuri kudin talakawa ba.

An dai sa ran cewa ko ma me yayi, Jonathan baza'a taba shi ba, saboda dattako da yayai bayan ya sha kaye a zaben 2015 daga Buhari na jam'iyyar adawa ta APC.

A bayanai na kotu a makon nan, wani hadimin shugaban yace shi da kansa ya kai wa shugaba Jonathan akalla Naira biliyan biyar uwar daki cikin wasu jakunkuna daga babban bankin CBN, kudade cikin dala da pam.

DUBA WANNAN: An kashe ma'aikatan UN a jihar Borno

A bayanai da yayi wa kotu a Legas dai, Mr. Orji Chukwuma yace akwatuna ne guda goma ne cif-cif ya karbo, kuma Jonathan yace a kai masa daka a ajiye masa.

Ana sa rai irin kudaden da ake kira security vote ne, wadanda ake amfani dasu ana bada cin hanci lokutan zabe.

Sai dai ba'a san ko Jonathan din zai fuskanci tuhumar gwamnati ba, ko kuwa su yaran nasa ne zasu ci gaba da shan wahala.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel