Satar malamai: Jami'ar Maiduguri ta sha alwashin cigaba da neman mai a tafkin Chadi

Satar malamai: Jami'ar Maiduguri ta sha alwashin cigaba da neman mai a tafkin Chadi

Jami'ar nan mallakin gwamnatin tarayya dake a garin Maiduguri, jihar Borno ta sha alwashin cigaba da hada gwuiwa da ma'aikatar hukumar rukunin kamfunan albarkatun man fetur na kasa watau NNPC wajen binciken da sukeyi na mai a tafkin Chadi.

Wannan dai ikirarin na mahukuntan jami'ar na zuwa ne kwanaki kadan bayan 'yan ta'addan Boko Haram sun sako manyan malaman jami'ar da suka yi garkuwa da su a watannin baya.

Satar malamai: Jami'ar Maiduguri ta sha alwashin cigaba da neman mai a tafkin Chadi
Satar malamai: Jami'ar Maiduguri ta sha alwashin cigaba da neman mai a tafkin Chadi

KU KARANTA: Bayahude yayi mafarkin Annabi ya musulunta

Legit.ng ta samu cewa da yake karin haske game da batun, mataimakin shugaban jami'ar Professor Ibrahim Njodi ya bayyana cewa duk wani tsoro ko razani ba zai yi tasiri ba a zukatan mahukuntan jami'ar kuma ma tuni har shire-shire sun yi nisa don ganin an cigaba da binciken.

A wani labarin kuma, Jami'in dan sandan Najeriya dake shiyyar jihar Akwa ibom a jiya Laraba ya lakadawa wani dan jarida mai suna Mista Samuel Ayara dukan tsiya a harabar majalisar dokokin jihar.

Kamar dai yadda labarin ya zo mana, dan sandan da ya bugi dan jaridar sunan sa Sunday Agada kuma yana aikin gadin dan majalisar jihar ne mai wakiltar karamar hukumar Ikot Abasi mai suna Mista Uduak Udoudo.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel