Alakar Diflomasiyya: Sakataren gwamnatin kasar Amurka zai kawo ziyara Najeriya

Alakar Diflomasiyya: Sakataren gwamnatin kasar Amurka zai kawo ziyara Najeriya

Sakataren kasar Amurka, Rex Tillerson zai kai ziyara zuwa Najeriya don ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a sati mai zuwa, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin sakataren kasar Amurka, Heather Nauert ta ce Tillerson zai ziyarci kasashen Adis Ababa, Djibouti, Nairobi da kuma N’Djamen, bayan ya kammala ziyarar Najeriya.

KU KARANTA: Wani abu guda ɗaya rak da Ganduje ke bukata daga Kwankwaso matukar yana son ayi Sulhu

A yayin ziyarar ta sa, ana sa ran Tillerson zai tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buharim tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Alakar Diflomasiyya: Sakataren gwamnatin kasar Amurka zai kawo ziyara Najeriya
trump

“A ziyarar sa ta farko zuwa nahiyar Afirka Sakatare Rex Tillerson zai kai ziyara N’Djamena, Chad; Djibouti, Djibouti; Addis Ababa, Ethiopia; Nairobi, Kenya da kumaAbuja, Nigeria, a tsakanin 6-13 ga watan Maris. Zai yi gana da shuwagabannin kasashen tare da shuwagabannin kungiyar kasashen Afirka, AU” Inji ta.

Sanarwar ta cigaba da fadin dallilin wannan ziyara na Tillerson shi ne don karfafa danganta tsakanin kasar Amurka da jama’an nahiyar Afirka, hala zalika zai tattauna da shuwagabannin kan hanyoyin magance matsalar ta’addanci, tare maido da zaman lafiya mai daurewa a Afirka.

Daga karshe sanarwar ta kara da cewa Tillerson zai gana da jami’an ofishin jakadancin Amurka dake wadannan kasashe, kuma zai shiga cikin duk wasu ayyuka da gwamnatin kasar Amurka ke gudanarwar a Afirka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel