Zaben 2019: Sabbin jam'iyyu 108 sun bukaci yin rijista a hukumar zabe

Zaben 2019: Sabbin jam'iyyu 108 sun bukaci yin rijista a hukumar zabe

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin gudanar da zabuka ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta ayyana cewa yanzu haka kungiyoyi 108 ne ke neman rijista a matsayin jam'iyyu kafin zaben 2019.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakub shine ya sanar da hakan a jiya Alhamis a yayin jawabin sa a wajen wani taro da yanzu haka ke cigaba da gudana na dandalin sada zumunta na mako daya watau 'Social Media Week'.

Zaben 2019: Sabbin jam'iyyu 108 sun bukaci yin rijista a hukumar zabe

Zaben 2019: Sabbin jam'iyyu 108 sun bukaci yin rijista a hukumar zabe

KU KARANTA: An kashe wani babban kwamandan sojojin Najeriya

NAIJ.com ta samu haka zalika cewa a cikin watan Disembar shekarar da ta gabata ma dai hukumar ta yi wa wasu kungiyoyin 21 rijista a matsayin jama'iyyu wanda ya kawo jumillar jam'iyyu a Najeriya yanzu ya zuwa 68.

A wani labarin kuma, Biyo bayan kin halartar manyan tarukan jam'iyyar APC mai mulki da shugaban majalisar dattijan Najeriya, Sanata Bukola Saraki yayi a farkon makon nan, kishin-kishin ta yawaita na cewar ko yana shirin ficewa daga jam'iyyar ne zuwa jam'iyyar sa ta PDP.

To sai dai wani babban hadimin sa mai taimaka masa ta fuskar yada labarai Mista Yusuph Olaniyonu ya bayyana cewa wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne domin shi Saraki din ba ya tsoron kowa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za a karrama gwamnoni 5 da suka fi yiwa jama’a aiki, duba bangaren da kowanne yafi dagewa

Za a karrama gwamnoni 5 da suka fi yiwa jama’a aiki, duba bangaren da kowanne yafi dagewa

Za a karrama gwamnoni 5 da suka fi yiwa jama’a aiki, duba bangaren da kowanne yafi dagewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel